Yau take Sallah a Nijeriyia

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Saad Abubakar
Image caption Mai alfarma Sarkin Musulmi, Saad Abubakar

Yau ne al'ummar musulmi a Najeriya da ma wasu kasashen ke yin bukukuwan sallah bayan kammala azumin watan Ramadhan. An gudanar da Sallar Idi a Sokoto, fadar Sarkin Musulmi a cikin wani yanayi na ruwan sama kamar da bakin kwariya.

Ruwan saman dai ya soma ne a daidai lokacin da masallatan da suka hada da mata da yara da kuma nakassasu suka hallara a Filin Sallar Idin dake wajen birnin Sokoto.

Sai dai wasu Musulman a wasu sassan Nijeriar da suka hada da wani yanki na birnin Sokoto, sun gudanar da tasu Sallar a jiya.