Musharraf ya bayyana shirin sake tsunduma ruwa a fagen siyasa

Pervez Musharraf
Image caption Pervez Musharraf, tsohon Shugaban Pakistan

Tsohon shugaban mulkin sojin kasar Pakistan Pervez Musharraf, ya ce yana hada wata sabuwar jamiyyar siyasar wadda za ta kai shi ga mulki a babban zaben kasar na shekarar 2013.

A lokacin da yake wata hira da BBC, tsohon janar din sojin ya bayyana cewa zai tsaya takarar majalisar dokokin kasar kuma yana fata zai zamanto Pirayim Minista ko kuma shugaban kasa.

Pervez Musharraf ya ce "na yi imani mai karfi da cewa, zai fi na kokarta na kasa, maimakon na ki yin wani hobbasa, na ci gaba da kasancewa a kasa. Saboda a yanzu ba abinda muke gani a Pakistan sai duhu. Dole mu samar da haske, mu samarwa yan Pakistan wani zabi, inda za su ga haske karshen duhun, su sami wani kwarin gwiwa".

Yayi watsi da sakamakon ra'ayin jama'ar dake nuna cewar bashi da kyakykyawar karbuwa-- ya ce,yayi ababuwa masu girma ga kasar Pakistan a matsayin Shugaban kasa, kuma goyon bayansa na kara karuwa.