Ra'ayi Riga: Yaya kuka yi bukin Sallar bana?

Sallar Idi
Image caption Sallar Idi

Kasashe da dama na duniya sun gudanar da bukukuwan Sallah karama, ciki har da Ghana, Kamaru da Najeriya - ko da yake wasu tun a jiya suka yi Sallar a Najeriyar.

A jamhuriyar Niger ma a jiya ne aka yi bukukuwan Sallar karama.

A kasashen, kamar dai a wasu sassa na duniya, an yi sallar ce a cikin wani hali na matsin tattalin arziki, wanda ya sa mutane da yawa ba su iya yin hidimomin da suka saba ba.

Baya ga haka kuma, akwai wasu matsalolin da suka taimaka wajen rashin armashin Sallar, irinsu annobar cutar kwalara da ambaliyar ruwa a wasu yankuna.

Baya ga wasu daga cikinku masu sauraro da suka tofa albarkacin bakinsu a cikin shirin, mun kuma gayyato wasu baki da suka hada da Alhaji Kabiru Hali, shugaban 'yan kasuwar jahar Sakkwato da Ibrahim Mohammed Alkasum, babban sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta jahar Kano, SERERA da kuma Sheik Moussa Sulaiman Alkahira.