Ambaliya na kara ta'azzara a Sokoto

Ambaliyar ruwa a wasu sassan Najeriya
Image caption Ana ci gaba da fuskatar ambaliyar ruwa a jihar Sokoto

Jama'a a jihar Sakkwato dake arewacin Najeriya, na ci gaba da fadawa cikin mawuyacin hali, sakamakon ambaliyar ruwa daga madatsar ruwa ta Goronya wadda wani sashe nata ya fashe a farkon makonnan.

Yanzu haka dai ruwa mai karfin gaske ya fara kwarara zuwa cikin wasu unguwannin babban birnin jihar, dake da tazarar kilomita saba'in daga madatsar ruwan, abinda ya tilastawa daruruwan mutane ficewa daga gidajensu.

Kazalika ruwan ya karya wata gada mai matukar muhimmanci a garin.

Ambaliyar ruwan dai ta yi sanadiyar rasuwar mutane da dama da kuma asarar kayayyaki a jihar.