Zanga zanga akan cibiyar Musulunci a Amurka

Daruruwan al'umma a birnin New York na Kasar Amurka sun yi ta faman nuna rashin amincewarsu dangane da shirin gina wata cibiyar Musulunci da za'a yi a kusa da filin cibiyar cinikayya ta duniya, wadda aka kai wa hari a shekarar 2001.

Duk da dai cewa zanga zangar ta lumana ce, amma a wadansu wuraren rahotanni na bayyana cewa an dan samu hargitsi.

Ana dai cigaba da jimami domin zagayowar ranar da dubban mutane suka rasu a harin da aka kaiwa cibiyar cinikayya ta duniya, ranar 11 ga watan Satumba.

Ga iyalan wadanda abin ya rutsa dasu, wannan shekarar tashin hankalin ya fi na baya muni.

Domin dai suna cike ne da fargabar barazanar kone Al- Qur'ani mai girma da wani fadan Coci wato Pastor Terry Jones ya yi, kan cewa a wannan ranar ne zai aikata haka, amma dai ya fasa.

Shugaba Obama dai ya nanata cewa sam Amurka ba za ta taba yakar addinin Musulunci ba.