Nuhu Ribadu ya ce 'yan Najeriya su kare kuri'unsu

Nuhu
Image caption Nuhu Ribadu

A Najeriya, tsohon shugaban hukumar dake yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati wato EFCC, Malam Nuhu Ribadu; yayi kira ga al'ummar kasar da su tabbatar sun kare kuri'unsu a lokacin zaben kasar da za'a yi a badi.

Ya kara da cewa muddin 'yan Najeriya suka kasa, suka tsare, su ka kuma raka kuri'un nasu, to tabbas akwai yiwuwar samun zabe mai inganci a kasar.

Ya dai yi wannan kiran ne a yayin wani taron wayar da kan jama'a da wata kungiyar 'yan Najeriya mazauna Amurka ta yi, a yankin Niger Delta.

Kungiyar mai suna United Nigeria Citizens Initiative (UNCI) ta gudanar da taron ne domin wayar da kan al'ummar yankin game da yadda za su kare kuri'unsu a lokacin zaben shekarar 2011.

Sai dai kuma wadansu a kasar na cigaba da bayyana shakkar cewa ko da 'yan Najeriyar sun kare kuri'un nasu, muddin jami'an zabe ba masu gaskiya ba ne, to akwai yiwuwar komawa gidan jiya.