Al'amura sun fara daidaita a Guinea

Kome ya koma daidai a Conakry Babban Birnin Guinea bayan artabun da aka yi jiya tsakanin yan bangaren jam'iyyun siyasar da ba sa ga maciji da juna, mako guda kafin zagaye na biyu na zaben Shugaban kasa.

Wani mai aikowa BBC rahotanni daga birnin na Conakry ya ce wasu masu fafutika na jama'iyun sun fita kan tituna, to amma babu dai wani karin tashin hankali.

Hukumar zabe na ganawa domin yanke shawarar ko ya Allah za a iya gudanar da zabe ranar lahadi mai zuwa.

Wakilin BBC ya ce a ranar juma'a ne dai aka yanke wa Shugaban Hukumar zaben da babban mai ba shi shawara kan tsare-tsare hukuncin daurin shekara daya a gidan maza bayan da aka same su da laifin magudi a zagayen farko na zaben a cikin watan Yuni.