Iran ta ce za ta iya sakin ba'amrukiyar da aka tsare

Kasar Iran ta ce a shirye take ta saki wata Ba'amrukiyar da aka tsare a kusa da kan iyaka da Iraqi fiye da shekaru biyu da suka wuce.

Wani mai gabatar da kara na kasar ta Iran, ya ce wata kotu ta baiwa matar, Sarah Shourd, belin dake tattare da sharadi na kusan dala dubu dari biyar saboda ba ta da lafiya. Jafari -Dowlatabadi ya ce, Iran na son taimakawa Ms Shourd.

An kama Ms Shourd ne tare da wasu Amurkawan maza biyu a cikin watan Yulin bara , aka kuma zarge su da leken asiri.

Amurkawan dai sunce suna balaguro ne, suka shiga cikin yankun kasar Iran bisa kuskure.