Kungiyar Amnesty ta ce ana cin zali a Iraqi

Image caption Gidan kaso a Iraqi

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta bayyana cewa cikin dubban mutanen da ake tsare da su a gidan kaso a Iraqi, ba tare da an yanke musu hukunci ba, har da wani dan Birtaniya.

A wani rahoto da ta wallafa a yau litinin, kungiyar Amnesty International din ta bayyana cewa daga sojojin Iraqin har da na Amurka na cin zarafin wadanda ake tsare da su a kasar.

Kamar yanda kungiyar Amnesty ta bayyana, fiye da shekaru bakwai tun bayan durkushewar gwamnatin marigayi Saddam Hussein, har yanzu ba a daina aikata wadansu munanan aiyukan ba.

Ramzi Shihab Ahmed, wani dan shekaru 68 dan Birtaniya, kuma dan Iraqi na tsare a wani gidan kaso tun watan Disambar bara.

An neme shi sama da kasa amma sam ba'a ganshi ba sai bayan da aka gano wani gidan kason sirri a watan Maris din da ya gabata.

Ya dai bayyana cewa an gana masa azaba, har ma da shake shi da kuma saka masa wuta a jikinsa.

A wani bincike da BBC ta yi a wancan lokacin, ta tabbatar da gaskiyar labarin.

Shi dai Mr. Shihab ya bayyana cewa saboda matukar azabar da ake gana masa, wanna ta sanya domin neman sauki, ya sanya hannu akan takardun shaidar cewa yana da alaka da kungiyar Al Qaeda.

Har yanzu kuma ana cigaba da tsare shi.

Wannan labarin kamar yanda kungiyar agajin bil adama ta Amnesty International ta bayyana, daya ne a cikin labarai masu dinbin yawa.

Kungiyar dai ta yi kiyasin cewa kimanin mutane dubu talatin ne ke tsare a gidan kason a Iraqi ba tare da an gurfanar dasu gaban kuliya ba, yayin kuma da wadansu ba'a yanke musu hukunci ba.

Kungiyar dai ta kara da cewa ana amfani ne da azaba iri iri domin sanya mutane su amsa laifin da basu aikata ba.

Wannan rahoton dai ya bayyana ne kasa da makwanni biyu kafin Amurka ta tarkata ya- nata- ya- nata ta fice daga Iraqin bayan kare aikin sojin da ta ke yi a can.

A watan Yulin bana ne kuma Amurka wadda itama sojinta dake Iraqin na da nasu kason dangane da azabtarwar, suka mika baki dayan ikon gidajen kason ga hannun jami'an Iraqi.

Wannan a cewar kungiyar Amnesty, ta yi ne ba tare da tunanin ko shin za'a tabbatar da cewa an kiyaye hakkokin fursunonin ba.