Kuri'ar raba-gardama a Turkiyya: Gwamnati ta yi nasara

Erdogan
Image caption Erdogan

Firaminista Recep Tayyip Erdogan ya ce gwamnati ta samu nasara yadda ta kamata a kuri'ar raba gardama a kan wani jerin sauye-sauye ga tsarin mulki.

Mr Erdogan ya ce kamar yadda sakamakon wucin gadi ya nuna, sauye sauyen -- domin dakile ikon soji da kuma sakewa bangaren shara'a fasali -- sun samu kusan kashi 60 cikin dari na karbuwa.

Ya ce, a yau dimukuradiyyar Turkiya ta kai wani matsayi. Wannan muhimmiyar shawara ce.

Gwamnatin Turkiya ta yi ta cewar ana bukatar sauye-sauyen domin karfafa dimukuradiyya.

To amma masu adawa na jin tsoron cewar za su baiwa gwamnatin Erdogan, mai tushen siyasar Islama, matsananciyar damar fada aji a kan kotuna.