Ana kada kuri'ar raba-gardama a Turkiyya

An fara kada kuri'ar raba-gardama a kasar Turkiyya kan wadansu sauye-sauye ga kudin tsarin mulkin kasar wadanda gwamnati ta gabatar.

Wadannan sauye-sauye guda 26 suna da goyon bayan Tarayyar Turai, kuma gwamnati ta gabatar da su ne ga jama'ar kasar a matsayin wani cigaba kan kudin tsarin mulkin kasar na 1982, wanda gwamnatin mulkin soja ta wancan lokaci ta kaddamar.

Sai dai jam'iyyar adawa ta kasar ta zargi gwamnatin da yin amfani da wannan gyaran fuska domin samun iko kan fannin shari'a, wanda a wasu lokuta yake kalubalantar matakan da jam'iyyar da take kan mulki ke dauka.