Afuwa ga masu fashi da kuma sace mutane a Najeriya

Image caption Za'a a yi shirin ne a kudu maso gabashin Najeriya

A Najeriya, sakamakon yadda ake ta fama da matsalar fashi da makami da sace mutane ana garkuwa da su don neman fansa a shiyyar kudu maso gabashin kasar, yanzu haka ana kokarin kaddamar da wani shiri na yin afuwa ga masu aikata wadannan miyagun laifuffuka a yankin.

Za a kuma fara da kaddamar da shirin ne a jihar Abiya, kana daga bisani ya karwade sauran jihohin shiyyar.

A bara ne dai aka fara kaddamar da irin wannan shirin na afuwa ga masu gwagwarmaya da makamai a yankin Naija-Delta, domin shawo kan matsalar sace-sacen jama'a ana garkuwa da su don neman fansar kudi da dai sauran miyagun laifuffuka.

Baya ga bin matakai irin na tsaro a kokarin shawo kan matsalar fashi da makami, da sace-sacen jama'a ana garkuwa da su don neman fansar kudi, wadanda suka zama wani babban alakakai a nan shiyyar kudu maso gabashin Najeriya, a yanzu hukumomin kasar sun kudiri aniyar amfani da shiri na musamman na yin afuwa ga masu aikata wadannan miyagun laifuffuka a wannan yanki.

An kafa kwamiti

Har ma an kafa wani kwamiti na musamman wanda ya kunshi jami'an 'yan sanda da sojoji da dai sauran wasu masu ruwa da tsaki, domin aiwatar da shirin afuwar.

Alhaji Hafizu Ringim, mukaddashin sufeto janar na 'yan sandan Najeriya, ya ce;

Image caption 'Yan sanda Najeriya na fama da fashin da makami da kuma sace mutane a kudancin kasar.

" Wannan shirin dama an taba yin irin ta a jihohin Niger Delta, yanzu dai gwamnatin tarrayar ta shirya cewa da wadanda ke fashi da kuma sace mutane domin karban fansa a jihohin Abia da Imo da Anambra da kuma Enugu, muna fatan wadannan mutane za su ajiye bindigoginsu domin su daina irin wadannan mugan ayyukan".

Wakilin BBC ya tambayi babban jami'in 'yan sandan Najeriyar, shin a gaba dayan shiyyar kudu maso gabashin Najeriya ne za a kaddamar da wannan shiri na afuwa ga masu aikata miyagun laifuffuka, ko kuwa daga wani waje za a fara daura dan ba?

Sai ya ce; " Zamu fara ne da Abia, amma duk wadanda ke sauran jihohin da ke irin wannan laifukan a sauran jihohin, idan sun amince za su bari, zamu yi maraba da su.

Alhaji Hafizu Ringim ya kuma ce, an tanadin hanyar kyautata rayuwar masu aikata miyagun laifuffukan, muddin suka mika kansu da makamansu ga shirin afuwar. Masu lura da al'amura dai na ganin bullo da wannan shiri ya dace. Sai dai kuma akwai bukatar gwamnatocin Najeriya su kara tashi tsaye, wajen kirkiro karin hanyoyin samun abin yi ga dubun dubatan matasan kasar, wadanda ke zaman jiran tsammanin samun wata madafa.