Ribadu ya koka da halin rashin doka da oda a Najeriya

Malam Nuhu Ribadu
Image caption Malam Nuhu Ribadu

Tsohon shugaban hukumar EFCC mai yaki da ma su yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, Malam Nuhu Ribadu, ya ce harkokin tsaro a kasar na kara tabarbarewa, ta yadda a yanzu suke neman su gagari hukumomi.

Malam Nuhu Ribadu ya bayyana hakan a birnin Badun na jahar Oyo, yayin da yake gabatar da kasida akan makomar Naijeriya, albarkacin wani taro da aka shirya domin tunawa da tsohon Atoni Janar, kuma ministan shari'a Cif Bola Ige, wanda aka hallaka a harin da aka kaiwa gidansa a birnin Badun, a watan Disamban dubu biyu da daya.

Taron ya zo ne a daidai lokacin da a Kano aka yi jana'izar wasu mutane biyar, 'yan gida guda, wadanda aka kashe a daren jiya.

Wasu mutane ne da ba a shaida ko su wanene ba suka shiga wani gida, a rukunin gidajen dake unguwar Kundila dake kan titin Gidan zoo, a cikin birnin Kano, inda suka yanka wani magidanci mai suna Garba Bello, mai kimanin shekaru hamsin da biyar, tare da matarsa da kuma 'ya'yansa ukku. Marigayi Garba Bello, mataimakin darakta ne a hukumar 'yansandan ciki ta Nigeria, wato SSS, wanda ke aiki a Sakkwato.

Rundunar 'yan sanda a Kano ta ce, kisan ba shi da nasaba da aikin fashi da makami, ya fi kama da kisan gilla.