An sabunta: 13 ga Satumba, 2010 - An wallafa a 13:32 GMT

Ta'aziyar wadanda aka yiwa kisan gilla a Kano

 • Ta'aziya
  A Nigeria anyi jana'izar mutanen wani gida da su biyar da aka yi musu yankan rago a daren ranar lahadi a jahar Kano.
 • Ta'aziya
  Wasu mutane da har yanzu ba'a san ko su waye ba sun shiga wani gida a rukunin gidaje dake unguwar Kundila a birnin Kano sun kashe wani magidanci Garba Bello mai kimanin shekaru hamsin da biyar da iyalansa.
 • Ta'aziya
  Garba Bello mataimakin darakta ne a hukumar yansandan ciki ta Nigeria, wato SSS wanda ke aiki a Sakkwato, an kashe shine da matarsa da kuma yayansu uku
 • Ta'aziya
  Rundunar yan sandan jahar ta Kano dai tace kisan bashi da nasaba da aikin fashi da makami, yafi kama da masu kisan gilla.
 • Ta'aziya
  Mutanen da aka kashe ta hanyar amfani da wuka bayan Garba Bello mai kimanin shekaru 55 sun hada da matarsa Habiba mai kimanin shekaru 40, sai Hafsa mai kimanin shekaru 17, da kuma Halifa mai shekaru 10 sai kuma Murja mai shekaru biyar.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.