An kashe mutane goma sha biyar a Kashmir

Tashin hankali a Kashmir
Image caption Tashin hankali a Kashmir

Akalla fararen hula guda 15 ne suka rasu, sannan da dama suka jikkata a yankin Kashmir dake karkashin ikon kasar India.

Hakan ya faru ne sakamakon zanga zangar dake ci gaba kan mulkin India a yankin, da kuma barazanar wata mujamiar Amurka ta kona Al-qura'ani.

Cocin dake Amurkar dai ba ta aiwatar da barazanar ta ta ba.

Yan sanda sun harba albarusai na gaske domin tarwatsa masu zanga zangar da dubban mutane suka yi a kwarin Kashmir a wurare daban daban inda suka rika rera taken nuna kin jinin Amurka da India.