Za a cigaba da tattaunawa a Gabas ta tsakiya

Image caption Tattaunawar yankin Gabas ta tsakiya

Ana saka rai da cewa tattaunawa tsakanin shugabannin Israela da Palasdinu ya taimaka wajen samar da zaman a yankin Gabas ta tsakiya.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton ma, za ta kasance a wurin tattaunawar, a wani yunkuri da Amurka ke yi na ganin cewa an cimma yarjejeniya.

Sai dai kuma akwai fargaba game da cewa dakatar da gina matsugunnan yahudawa ya iya sake janyo wata matsalar.

Su dai Palasdinawa sun yi gargadin cewa sam babu amfani cigaba da magana tsakaninsu da Israela muddin Israelan ba ta daina gine- gine ba.

Shi kuma Prime Ministan Israela ya bayyana cewa sam ba shi da niyyar dakatar da gine- ginen, amma dai ya yi alkawarin takaitawa.

Alamu na nuni da cewa ba bu wanda zai iya bayar da kai domin bori ya hau, musamman ma a wannan dan gajeren lokacin.

Sai dai kuma abu ne mai wahala a iya tunanin cewa tattaunawar za ta watse nan da nan, musamman ma idan aka yi la'akari da irin jan aiki da kuma yunkurin siyasar da gwamnatin Amurka ke yi akan ganin an samu maslaha.