An saka sabbin dokoki a bankunan duniya

Image caption Birnin Basel na Switzerland

Manyan bankunan kasashen duniya da cibiyoyin dake sa ido akan ayukan bankunan sun amince da wasu sabbin sauye-sauye da zasu hana sake aukuwar irin rudanin da tattalin arzikin duniya ya fuskanta a shekara ta 2008.

An amince ne da wadannan sauye sauyen a wurin wani taro da aka yi a birnin Basel na kasar Switzerland.

Muhimmi sauyin da aka amince da shi a cikin sabbin sauye-sauyen shine, tsarin nan da ya bukaci bankuna, a koda yaushe su kansance suna da isassashen jari sosai, ta yadda za su kai labari koda kasuwar hada-hadar kudi ta fuskanci wata tangarda.