Kudaden Fensho na taimakawa tattalin arziki

A kasashen duniya da dama tsarin pensho na cikin abubuwan dake taimakawa wajen rage talauci musamman a tsakannin tsofaffin da suka haura shekaru 60 (sittin) da haihuwa.

Sai dai kamar yadda hukumar kwadago ta duniya wato ILO tace, daya daga cikin kowanne ma'aikata (5) biyar ne kawai ke karbar kudin fensho.

Babban bankin duniya kuma ya ce kashi 85 bisa dari na al'ummar duniya basa karkashin fensho, ko kuma wani tanadi da suke dogaro dashi wajen tafiyar da rayuwarsu bayan ritaya.

NIGERIA:

A Najeriya, kusan shekaru shida kenan da gwamnati ta fito da sabbin dokoki na tsarin fensho a kasar.

Manufar tsarin dai shi ne, inganta yadda ake biyan wadanda suka yi ritaya daga aiki hakkokinsu cikin sauki, ganin irin matsalolin da suka yi ta faruwa a baya.

A wani bangare na aiwatar da dokar ne aka kafa hukumar pensho ta kasa wadda ke da alhakin sa ido wajen ganin cewa an biya ma'aikatan kasar hakokinsu na fensho akan lokaci.

Wani kiyasi da hukumomin Najeriya suka yi na nuni da cewa kimanin mutane miliyan hudu ne suka yi rejista da wannan sabon tsarin.

Sai dai kuma duk da cigaban da gwamnatin Najeriya ke ikirarin samu a wannan sabon tsarin fenshon, masana a wannan bangaren sun bayyana cewa akwai bukatar hukumomi su kara kaimi wajen wayar da kan jama'a, musamman ma idan aka yi la'akari da cewa kimanin kashi saba'in cikin dari na al'ummar kasar ba su yi rejista ba.

GHANA:

A Ghana ma masu karban fensho na da nasu matsalolin daban daban.

Wannan kuma ya danganta ne da karkashin irin tsarin fenshon da mutun ya fada.

Da ga cikin nau'o'in fenshon da ake dasu a kasar, sun hada da tsarin fenshon na Cap 30 wanda ya shafi sojoji da sauran jami'an tsaro.

Sai kuma na Social Security and National Insurance Trust wato SNNIT wanda ya shafi sauran ma'aikatan gwamnati. A karkashin wadannan tsare- tsaren, ana fara biyan mutunin da ya yi ritaya jimillar kudade, sannan a kowanne wata za a biya kimanin rabin albashin da ya saba karba kafin yayi ritaya.

To sai dai bababr matsalar da masu karbar fenshon ke fuskanta itace; duk mutumin da ya yi ritaya dole ne sai ya je ofishin kula da fenshon ma'aikata wato Penshion House dake birnin Accra, domin a lissafa ma sa kudin fenshon sa kafin ya fara karba.

Amma saboda tsananin talauci, kudin motar zuwa babban birnin kasar kan yi wa mutane wahala, hakan kuma kan sanya wasu har su mutu ba su karba ba.