Yau ce ranar demokradiyya ta duniya

Yau ce ranar Dimokradiyya ta duniya.

Majalisar Dinkin Duniya ta ware wannan ranar ne domin yin nazari a kan halin da tsarin dimokradiyya ke ciki a fadin duniya.

Tun a shekarar 2007 ne Babban Zauren Majalisar ya ware ranar 15 ga watan Satumbar na kowacce shekara, domin karfafawa gwamnatoci da kungiyoyin al'umma gwiwa wajen inganta dimokradiyya.

Wanann ne karo na uku da ake bukin ranar, inda Majalisar dinkin duniya kan gayyato kasashe da kungiyoyi domin yin waiwaye adon tafiya, don tantance irin ci gaban da tsarin dimokradiyya ke samu a duniya.

Majalisar dinkin duniya ta bayyana tsarin dimokradiyya a matsayin hanyar samar da ci gaban al'umma da kuma samun 'yan cin bil adama a fadin duniya.

Kamar yanda masana harkar siyasa ke bayyana wannan ranar, sun ce dimokradiyya tsari ne na mulkar kai, wanda ya baiwa al'umma damar zaben abinda su ke so.

Malam Abubakar Kari wani masani a jami'ar Abuja a Najeriya, ya bayyana cewa daga cikin dalilan da suka sanya Majalisar dinkin duniya ta ware wannan ranar shine domin tabbatar da gaskiya da adalci a duniya.

Sai dai kuma Majalisar dinkin duniya na ganin cewa tsarin mulkin dimokradiyyar na fuskantar barazana iri- iri a wasu sassa na duniya.

Daga cikin barazanar har da jahilci da rashin bin doka da oda, da kuma rashin shugabanci na gari.