Ghana zata kauce ma dogaro da man petur

A kasar Ghana, yayin da kampanonin hako danyen man petur ke ci gaba da gano karin rijiyoyin danyen man a wasu sassan kasar, gwamnati ta ce zata yi amfani da kudaden da zata samu daga arzikin man wajen janyo hankalin masu saka jari daga kasashen waje.

Gwamnatin ta ce zata yi hakan ne, domin su zuba jari a wasu fannonin daban ta yadda kasar ba zata dogara kan arzikin danyen man kawai ba.

Mataimakin shugaban kasar, Mr. John Mahama ne ya fadi hakan a karshen wata ziyarar aiki da ya kai a kasar China.

An dai kiyasta cewa adadin danyen man da kasar ta Ghana take da shi a karkashin kasa ya kai sama da ganga miliyan dubu guda da rabi.