Shugaban soji na Nijar na ziyara Najeriya

Image caption Shugaban Soji na Nijar

Shugaban gwamnatin Soji na Jamhuriyar Nijar Manjo Salou Djibou na wata ziyara a Najeriya domin halartar wani taro na shugabannin kasashen da Kogin Kwara ya ratsa su.

Sai dai ana ganin cewa duk da Shugaba Djibou ya yi wannan ziyarar ne domin halartar taron da za a yi a yau a babban birnin tarayya Abuja, mutane da dama na ganin cewa zai yi amfani ne da wannan damar wajen neman goyon bayan shugabannin kasashen, musamman ma wajen ganin kasar sa ta koma kan tafarkin dimokradiyya.

Akwai yiwuwar cewa shugaban zai nemi goyon bayan sauran shugabannin da ke halartar taron, dangane da hukuncin da kotun kungiyar ECOWAS ko CEDEAO za ta yanke akan karar da magoya bayan tsohon shugaban kasar Malam Mammadou Tandja su ka shigar.

An dai shigar da karar ne a gaban kotun bisa ga neman fayyace ko shin cigaba da tsare tsohon shugaban da gwamnatin sojin Nijar din ke yi ya saba da ka'ida.