Kafin samun yan cin kai

Image caption Masu rike da sarautun gargajiya kafin samu 'yancin kai a wani taro

Turawan Potugal su ne wadanda suka fara harkar kasuwanci a Najeriya a tashar ruwan da suka baiwa suna Lagos da ta Calabar a karni na 17 zuwa na 19.

Turawan sun rika shigo da kayayyakin kasuwanci suna musayarsu da bayi a wannan lokaci wanda shugabannin al'ummar wuraren ne kadai ke mu'amala da su kuma ke ribanta daga cinikin.

A shekarar 1807 Burtaniya ta dakatar da cinikin bayin da take a Najeriya, kuma biyowa bayan yake-yaken rububin mallakar kasashe, Burtaniya ta kafa wata runduna a Afirka ta Yamma a wani yunkurin dakatar da cinikin bayi da kasashen duniya ke yi.

A shekarun 1884 zuwa 1885, aka gudanar da wani babban taro a kasar Jamus da ake kira da Taron Berlin, inda aka kakkasa kasashen Afirka zuwa yankuna daban-daban na mulkin mallaka.

Bayan taron, Burtaniya ta samu yankuna da dama a Yammacin Afirka, wanda Najeriya na daga ciki.

Har zuwa wannan lokaci ikon Turawan mulkin mallakar bai karasa Arewacin Najeriya ba, yawanci ikonsu ya karkatane a kudancin kasar da kuma yankin Ikko ko Legas.

A shekarar 1903, Turawan sun samu nasarar mamaye Arewacin Najeriya bayan tabka gumurzu tsakanin su da sarakunan daular Usmaniyya, wannan ne ma ya yi sanadiyyar rasuwar marigayi sarkin Musulmi Attahiru.

Turawan Mulkin mallakar sun cafke sarakuna kamar sarkin Kano Alu bayan da yaki mika wuya, inda suka kulleshi a Lokoja.

Bayan wannan ne kuma Turawan suka samu mallakar yankunan biyu da yankin Ikko.

A shekarar 1914, babban gwamna janar Fredrick Lugard ya hade yankunan kudu da Arewa aka sa wa kasar suna.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Suna

Sunan Najeriya ya samo asali ne daga kogin Neja bayan da a ranar 8 ga watan Janairu na shekarar 1897, wata 'yar jarida wadda daga baya Fredrick Lugard ya aura, Dame Flora Louisa Shaw, ta rubuta wata kasida a jaridar "The Times" ta Ingila kan cewa ya kamata a sawa kasar suna Nijeriya wato "Niger da Area", sabilida kogin Neja da ya bi ta cikin kasar.

Najeriya na makwabtaka da kasar Benin, ta Yammaci, Chadi da Kamaru ta Gabashi da kuma jamhuriyar Nijar da Arewaci.

Baki dayan kasashen da Najeriya ke makwabtaka da su Faransa ce ta mulkesu, in banda Arewacin Kamaru da Burtaniya ta mulka zuwa wani lokaci kafin Faransar ta karba.

Tun daga wannan lokacin Burtaniya ta rika gudanar da mulkin mallaka karkashin tsarin mulkinta wanda ke da majalisar dokoki da ta kunshi yan kalilan daga cikin yan Najeriya.

Da tafiya tai tafiya an nada wasu yan Najeriya da su shugabanci wasu yankunan kasar.

Wannan ya ba su karin ikon cin gashin kai, sai dai kuma hakan shi ne ummul aba'isin haifar da rikice rikicen addini da na kabilanci a sassa daban daban na Najeriyar.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Bayan da Turawan suka ga lamarin ya ki ci ya ki cinyewa sai sukai tunanin sake fasalta kasar, inda suka kasa ta zuwa yankuna uku, kabilar Yarabawa a Yammaci, Hausa da Fulani a Arewaci sai kabilar Ibo a Gabashin kasar.

Kodayake wannan tsarin ya raba 'yan kasar, to amma kuma kowanne bangare ya samu karfin fada aji a yankinsa.

Bayan da wadannan manyan kabilun uku na Najeriya suka samu karfin mulkar jama'arsu, nan da nan sauran kananan kabilun kasar ma suka fara neman da a basu yancinsu inda akai ta rikici.

Domin a samu kwanciyar hankali a shekarar 1954, an cimma wata yarjejeniyar rarraba ikon tafiyar da ayyukan ci gaban al'umma da ci gaban kasa kamar kiwon lafiya, ilimi da dai sauransu, a tsakanin kabilun kowane yanki.

Ita kuma gwamnatin kasa ke kula da harkokin tsaro da tattalin arziki.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kodayake wannan bai kawo karshen rikicin ba har sai da aka kafa wata hukuma 1957 mai suna Willink Minorities Commission, wadda ta duba korafe-korafen kananan kabilu a wannnan lokacin.

A shekarar 1953, Chief Anthony Enahoro ya gabatar da wani kudiri a majalisar dokoki na baiwa Najeriya 'yancin kai a shekarar 1957.

Sai dai kuma 'yan Arewacin Najeriya basu amince da hakan ba saboda karancin kwararru da za su tafiyar da harkokin mulki a yankin, da kuma gudun cewa yan kudancin kasar za su mamaye harkokin gwamnati.

To a wannan lokacin ne aka yi ta tura 'yan Arewa kasashen turai musamman Ingila domin yin kwasa-kwasai ta yadda za su samu ayyuka kamar su akawu da akanta.

To domin samun zaman lafiya bisa wadannan banbance-banbance ne aka amince da shekarar 1960 da za'a ba Najeriya 'yancin kai.