Takaitaccen tarihin Aguyi Ironsi

Aguyi Ironsi
Image caption Janar Aguyi Ironsi

An haifi manjo janar Johnson Umunnakwe Aguiyi-Ironsi ranar 3 ga watan Maris, 1924 a garin Umahia-Ibeku wato jahar Abia a yanzu.

Ironsi ya girma a hannun yayarsa ne wadda ta auri wani dan kasar Saliyo wato Theophilius Johnson.

A watan Fabrerun shekarar 1942 ne Aguiyi-Ironsi ya shiga aikin soji wato yana dan shekara 18.

Ironsi ya samu horan soji a Ingila, inda ya kai matakin Laftanal a shekarar 1949. Daga bisani ya dawo Najeriya inda aka bashi matsayin mai tsaron lafiyar gwamna Janar na Najeriya a wancan lokaci, John Macpherson.

Aguiyi-Ironsi ya yi fice a aikin soji, abinda ya sa ya yi takarar neman mukamin kwamandan rundunar sojin Najeriya, wanda gwamnatin hadin guiwa ta NPC da NCNC suka amince a bashi mukamin, kuma ranar 9 ga watan Fabrerun shekarar 1965, Ironsi ya zamo kwamandan rundunar sojin Najeriya.

Aguiyi-Ironsi ya mulki kasar a matsayin shugaban kasa na tsawon watani shida kafin wasu sojojin su yiwa gwamnatinsa juyin mulki.

29th July 1966: Zafin kisan shugabannin da aka yi musamman na Arewa a lokacin juyin mulkin da Ironsi ya dane shugabanci ne yasa wasu sojojin suka taso domin yiwa gwamnatinsa juyin mulki.

A lokacin da ya kai ziyarar rangadi yankin Yammacin Najeriya wanda gidan gwamnatinsa ke Ibadan, a daran wannan rana Aguiyi-Ironsi ya ji kishin-kishin cewa sojoji na shirin yi masa juyin mulki, inda da sanyin safiyar 30 ga watan Yuli, sojojin karkashin jagorancin Theophilus Danjuma suka yiwa gidan gwamnatin da ya kwana a ciki kawanya, inda Danjuma ya ma sa tambayoyi game da juyin mulkin da yakai ga kisan Sardaunan Sokoto, Sir Ahmadu Bello.

Daga bisani an tsinci gawar Aguiyi-Ironsi da gwamnan soji a yankin Yammacin Najeriya, Laftanal Kanal Adekunle Fajuyi a wani daji dake kusa da garin Badin.