Janar Babangida ya kaddamar da kamfe

Image caption Janar Ibrahim Badamasi Babangida

A Najeriya a yau ne tsohon shugaban mulkin sojin kasar Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya kaddamar da kamfen din neman tsayawa takarar shugaban kasa karkashin jamiyyar PDP mai mulkin kasar.

Gangamin wanda aka kaddamar a Abuja ya sami halartar wasu gwamnonin jahohin kasar uku.

Gwamnonin PDP sun hada da na jahohin zamfara, Mamuda Aliyu Shinkafi da na jahar Niger, Mu'azu Babangida Aliyu da kuma gwamnan Adamawa, Murtala Nyako.

Haka kuma wasu manyan 'yan siyasa wadanda suka rike manyan mukamai daban daban a najeriyar sun halarci taron, inda aka gudanar da jawabai daban daban a yayin gangagamin.

To sai dai taron na zuwa ne daidai lokacin da ita ma jamiyyar PDP ta ke gudanar da taron majalisar zartarwarta a yau, kuma shugaban kasar, Goodluck Jonathan ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takara a shafinsa na facebook.