Takaitaccen tarihin Ernest Shonekan

Ernest Shonekan
Image caption Ernest Shonekan

An haifi Ernest Adegunle Oladeinde Shonekon ranar 9 ga watan Mayun shekarar 1936 a Ikko ko legas, inda yayi yawancin rayuwarsa.

Cif Shenakon ya yi karatu a makarantar CMS grammar School, sannan yayi karatun digirinsa a jami'ar Landan a fannin shari'a.

A shekarar 1964 ya kama aiki da kamfanin UAC kuma daga bisani aka tura shi makarantar koyan kasuwanci ta Harvard domin ya samu karin horo a fannin kasuwanci.