Faransa ta mayarwa da Tarayyar Turai martani

Gwamnatin Faransa ta sake maida martani cikin fushi game da sukar da hukumar tarayyar turai tayi mata game da Korar Romawa da Faransar ke yi daga cikin kasarta.

Ministan kula da harkokin tarayyar turai na Faransar Pierre Lellouche ya yi kakkausan kalamai ga kwamishiniyar kula da harkokin shari'ar tarayyar turai Viviane Reding wadda ta kwatanta korar Romawan, da muzgunawar da kauyawa suka fuskanta daga wurin yan Nazi lokacinda suka mamaye Faransa a yakin duniya na biyu.

Ya ce a matsayina na minista a Faransa, kuma da ga wanda yayi yaki domin 'yantar da Faransa, ba zan bari Ms Reding ta kwatanta Faransar shekara ta 2010, don yadda ta tunkari alamuran Roma, da Faransar Vichy ba.

Bai kamata a yi maganar yakin duniya na biyu ba.