Goodluck Jonathan ya ce zai tsaya takara

Image caption Shugaba Jonathan ne dan kudu na farko a jam'iyyar PDP da ya bayana aniyarsa na tsayawa takara.

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben shekarar 2011 a shafinsa na sada zumanta na Facebook.

Jonathan ya kuma bayyan ranar Asabar mai zuwa 18 ga watan Satumbar da muke ciki da cewar ranar da zai fito fili ya bayyanawa jama'a a hukunce cewa zai tsaya takarar shugabancin kasar.

Bayyana aniyar ta shugaba Goodluck a shafin Facebook na zuwa ne a dai dai lokacin da tsohon shugaban Najeriya Janar Ibrahim Babangida ke kadamar da bikin bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben na badi.

Shugaba Jonathan ya ce watanni hudu da darewa karagar mulki bayan rasuwar Shugaba Yar'adua, ya dukufa ne wajen aiwatar da shirye-shirye na cigaba da za su inganta rayuwar al'ummar kasar.

Ya ce zai tsaya takara ne bayan jama'a da dama a fadin kasar sun nemi da ya yi hakan saboda kyawawan manufofin da gwamnatinsa ta shimfida.

Shugaba Jonathan ya ce bayan ya tattauna da bangorori dabam-daban a fadin kasar, sun bashi goyon bayan da ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2011, domin cigaba da ayyukan da gwamnatinsa ke yi.

Shugaban kasar dai ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da gwamnatinsa ta samu cikin watanni hudu da ya karbi shugabanci kasar a shafinsa na Facebook, wadanda suka hada da inganta tattalin arzikin kasa da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Tsarin karba-karba na PDP

Shugaba Goodluck Jonathan shi ne dan kudu na farko da ya fito ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a jam'iyyarsa ta PDP, kuma masu lura da al'amuran siyasa na ganin zai fuskanci kalubale a jamiyyarsa ta PDP wanda ke bin tsarin karba karba.

A tsarin Jam'iyyar PDP, arewacin kasar ce za ta ci gaba da mulki na tsawon shekaru hudu, bayan shugaba Yar'adua ya rasu a kan mulki a wa'adin mulkinsa na farko.

A baya dai tsohon shugaban kasa cif Olusegun Obasanjo wanda dan kudu ne, ya yi mulki na tsawon shekaru takwas, inda kuma Jam'iyyar ta ce arewacin kasar ce za ta yi nata shekara takwas din.

Jam'iyyar PDP dai har wa yau ta ce shugaba Jonathan na da 'yancin tsayawa takara domin ya ci gaba da wa'adin marigayi shugaba 'Yar'adua.

A yanzu haka tsohon mataimakin Shugaban kasar Atiku Abubakar da tsohon shugaban mulkin soji janar Ibrahim Babangida sun nuna aniyarsu ta tsayawa shugabancin kasar.