Takaitaccen tarihin janar Ibrahim Baban gida

Janar Ibrahim Badamasi Babangida
Image caption Janar Ibrahim Badamasi Babangida

An haifi janar Babangida ranar 17 ga watan Agusta na shekarar 1941 a garin Minna na jahar Neja.

Ya yi karatu a makarantar soji ta India a shekarar 1964, makarantar horas da sojoji ta Royal Armoured Centre ta Ingila daga 1966, kwalejin sojoji ta Jaji a shekarar 1977 da kuma makarantar sojin ruwa ta Amurka a shekarar 1980.

A shekarar 1962 ya shiga aikin soji inda yai aiki a gwamnatin sojin janar Obasanjo. Ya taka rawar gani a juyin mulkin 1976.

Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi aure ranar 6 ga watan Satumbar 1969 ga Maryam wadda Allah ya yiwa rasuwa ranar 27 ga watan Disambar 2009. Janar Babangida na da 'ya'ya 4 biyu maza biyu mata.