Takaitaccen tarihin Janar Olusegun Obasanjo

Janar Olusegun Obasanjo
Image caption Janar Olusegun Obasanjo

An haifi janar Obasanjo ranar 5 ga watan Maris na shekarar 1937 a garin Abeokuta na jahar Ogun.

Ya shiga aikin soja a shekarar 1958, inda ya samu horon soji a makarantar sojoji ta Aldershot.

A lokacin yakin basasar Najeriya, janar Obasanjo, ya jagoranci rundunar sojojin ruwa ta 3 wadanda suka kwato Owerri daga hannunun rundunar sojin Biafra, abinda yasa suka mika wuya har aka kawo karshen yakin.

Duk da cewa kai tsaye bai takarawa ba a juyin mulkin da janar Murtala ya jagoranta a shekarar 1975, amma dai dari bisa dari ya goyi bayansa, inda bayanda janar Murtala ya hau kan mulki aka bashi mataimakinsa.

Kundin tsarin mulkin da aka amince da shi a shekarar 1979, ya fito da tsarin shugabanci irin na Amurka wato mai shugaban kasa da mataimakinsa da kuma majalisar dattawa da ta wakilai.

Kuma kan hakane aka gudanar da zabe a wannan shekarar, inda a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1979, janar Obasanjo ya mika mulki ga Alhaji Shehu Shagari.

Janar Obasanjo ya kasance shugaban soji na farko a Najeriya da ya mika mulki ga fafar hula cikin lumana.

Obasanjo ya tsaya zabe a shekarar 1999 inda ya lashe zaben shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

Obasanjo ya sauka ne daga kan mulki a shekarar 2007, bayan ya kammala wa'adi biyu a kan karagar mulki.