Kwamitin zartaswa na PDP ya kammala taro a Abuja

Shugaban jam'iyyar PDP, Dr E. Nwodo
Image caption Shugaban jam'iyyar PDP, Dr E. Nwodo

A Najeriya, kwamitin zartaswar jam'iyyar PDP mai mulkin kasar ya yanke shawara kan jadawalin zaben fitar da gwani na jam'iyyar.

A karshen wani taron gaggawa da kwamitin na ta ya yi a Abuja, jam`iyyar ta amince da cewa za ta fara ne da zaben `yan majalisar jihohi daga ranar biyu ga watan Oktoba, kana a yi na gwamnoni daga ranar shida zuwa takwas ga Oktoba, na majalisar dokoki na kasa kuma daga sha biyu zuwa sha biyar ga watan oktoba yayin da za ta kammala da na shugaban kasa daga ranar sha takwas zuwa ashirin ga watan oktoba.

Wannan tsarin dai ya saba da wanda hukumar zaben kasar ta bayar, wanda ya bukaci a fara da zaben `yan majalisun dokokin na kasa da na shugaban kasa kafin a yi na gwamnoni.