Juyin mulkin shekara ta 1983

Janar Mohammadu Buhari
Image caption Janar Mohammadu Buhari

Wannan shi ne juyin mulki na 4 da sojoji sukai tun bayan da Najeriya ta samu ‘yancin kai daga Turawan mulkin mallaka a shekarar 1960.

Batun magudin zabe da ake zargin an tabka da kuma tabarbarewar tattalin arzikin da kasar ta shiga na daga cikin dalilan da sojojin suka bayar na karbe mulki daga hannun farar hula, duk da irin dangantaka ta kud-da-kud da suke da ita da gwamnatin.

Bayan juyin mulkin sojojin sun nada mutumin da ya jagoranci juyin mulkin wato Janar Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa.

Da hawansa mulki, janar Buhari ya yi kokarin maido da gaskiya a tsakanin ma'aikata tare da farfado da tattalin arzikin Najeriya ba tare da taba tsarin gwamnatin ba.

An kafa kotunan sojoji domin kawarda cin hanci, ina aka dinga bankado abubuwa da dama.

Wannan yasa aka sake tankade da rairaye ma'aikatun gwamnati, ko da yake bai kai yawan wanda akayi ba a shekarar 1975 ba.

Wani karin mataki da janar Buhari ya dauka na kawo gyara tsakanin ma'aikatu da jama'a shi ne na kaddamar da Yaki da Rashin Da'a wato War Against Indiscipline ko WAI a shekarar 1984, wanda ya hada da aiki cikin gaskiya, kishin kasa, tsabtace muhalli, da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Shirin bai cimma burinsa ba kamar yadda aka so, domin kuwa rashin aikin yi tsakanin jama'a a kasar ya karu yayin da tabarbarewar tattalin arziki ta dada kamari.

Wata babar matsala da gwamnatin sojin janar Buhari ta fuskanta ita ce ta bashin da ake bin Najeriya, inda ta gaza cimma daidaito da bankin bada lamuni na duniya wato IMF kan lokacin da zata biya, kuma a karshe bankin ya gindayawa Najeriya wasu sharuda na tsuke bakin aljihunta.

Har ila yau gwamnatin janar Buhari ta dauki matakin zabtare yawan sojoji a wannan lokaci. Duka wadannan matsalolin sun janyowa gwamnatin bakin jini a wurin jama'a.

Don haka cikin watan Agustan shekarar 1985, wasu sojoji galibinsu ‘yan Arewa karkashin jagorancin janar Ibrahim Babangida suka hambarar da gwamnatin janar Muhammadu Buhari.