Takaitaccen tarihin Yakubu Gowon

Image caption Janar Yakubu Gowon

An haifi janar Yakubu Gowon ne a garin Pankshin na Jos jahar Plato, ranar 19 ga watan Oktoban shekarar 1934.

Janar Gowon ya yi karatunsa a garin Zariya a jahar Kaduna, inda daga bisani ya shiga aikin soji.

Ya samu horan soji a kasar Ghana da Ingila, sau biyu kuma ya yi aiki a kasar Congo a rundunar wanzar da zaman lafiya ta Najeriya a kasar.

Janar Gowon ya yi gudun hijira zuwa kasar Burtaniya, kuma an sauke shi daga mukaminsa bisa zargin sa da hannu wajen kashe wanda ya gaje shi wato janar Murtala Ramat Muhammed a shekarar 1976.

A shekarar 1981 Alhaji shehu Shagari yai masa afuwa, sannan kuma a shekarar 1987, a lokacin mulkin janar Ibrahim Badamasi Babangida akai mayar masa da mukaminsa na soji.

Janar Yakubu Gowon ya yi karatun digirinsa na 3 wato Ph.D a jami'ar Warwick a Burtaniya, ya kuma zama Farfesa a jami'ar Jos.

Yanzu haka Janar Yakubu Gowon ya zama daya daga cikin dattawan Najeriya.