An samu gawar wata mata bayan bacewar ta a Maradi

Matsalar tsaro a jahar Maradi na dada tayar da hankalin mutanen yankin, bayan da aka yi yunkurin satar wata mata a makon daya gabata a garin Maradi.

A wannan karon a wani gari mai suna Maigero dake yankin madarunfa wata mata ta bata wacce aka samu gawar ta kwana daya bayan bacewar ta.

An gano cewa dai matar ta mutune sakamakon wani mutum da ba'a san ko wannene ba ya sassare ta da adda .