Rashin tsaro a Najeriya ya addabi gwamnati

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Image caption Kungiyoyin dake da ruwa da tsaki a harkar tsaro a Najeriya sun hadu domin nemo bakin zaren rashin tsaron dake neman tabarbarewa a cikin kasar

A Najeriya ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta shirya wani taro a kan matsalolin da ke damun kasar da suka hada da sace-sacen mutane don neman kudin fansa ,da kashe-kashen jama'a da ake dangantawa da siyasa.

Jami'an hukumomin tsaron kasar daban-daban da kuma kwararru ne aka gayyata domin su ba da shawarwari a kan yadda za a shawo kan matsalolin.

Harkar tsaro dai na ci gaba da tabarbarewa a Najeriyar. Ko da a makon nan an ba da labarin kisan gillar da aka yi wa wasu jami'an tsaron kasar

Malam Muhammad Ahmed, wani Jami'i a ma'aikatar harkokin cikin gida ta Najeriya, ya shaidawa BBC cewar taron ya hada kungiyoyin dake da ruwa da tsaki a harkar tsaron kasar domin nemo bakin zaren matsalar

Wasu mahalarta taron sun bayyana cewar samarwa da matasa ayyukan yi na daga cikin irin matakan daya kamata abi wajen magance wannan matsala.