Fafaroma Benedict ya isa Burtaniya

Paparoma Benedict
Image caption Paparoma Benedict

Jagoran Cocin Roman Katolika, Fafaroma Benedict ya isa Edinburgh don fara ziyarar aiki.

yerima Phillip mijin Sarauniya Elizabeth ne ya tarbi Fafaroman a filin saukar jiragen sama na birnin na Edinburgh, to amma babu wani buki da aka a gudanar a hukumance.

Ziyarar kwanaki hudun Fafaroman a Birtaniya za ta fara ne da wata ganawa a asirce da Sarauniyar Ingila a fadarta ta Holyroodhouse.

Bayan wata liyafa a farfajiyar fadar, Fafaroman zai ratsa titunan birnin Edinburgh a motarsa ta musamman, a wani jerin gwano na addini.

Fafaroma Benedict dai na fatan wannan ziyara tasa za ta taimaka wajen farfado da akidun addinin Kirista a kasar Burtaniyar, wadda ke kara yin nesa da addini.

Fadar Fafaroman ta Vatican dai ta yi shakulatun bangaro da rashin amincewar da wadansu mutane ke nunawa da wannan ziyara.

Wadanda ke suka a kan makudan kudaden da za a kashe yayin ziyarar da kuma wadanda badakalar lalata da kananan yara da ake zargin wadansu limaman cocin da aikatawa ta fusata su ne dai suka nuna adawa da ziyarar.

Karin bayani