Ana zabukan 'yan majalisa a Afghanistan

Daya daga cikin sojojin da ke ba da tsaro a Afghanistan
Image caption An tsaurara matakan tsaro yayin gudanar da zabukan

A yau ne masu kada kuri'a a Afghanistan ke zaben sabuwar majalisar dokokin kasar.

Za a gudanar da zabubbukan ne dai cikin fargaba sakamakon barazana daga 'yan Taliban.

Ana kallon wadannan zabuka a matsayin zakaran gwajin dafi ga halalcin gwamnatin Afghanistan, saboda matsalolin da suka biyo bayan zaben Shugaba Hamid Karzai a karo na biyu bara.

Kungiyar Taliban din dai ta yi barazanar hana zabubbukan gudana, kuma har ta harba rokoki a kan babban birnin kasar, wato Kabul.

An dauki tsauraran matakan tsaro, inda aka girke dubban sojojin Afghanistan da na kasashen waje a wadansu muhimman wurare.

Masu kada kuri'ar dai za su zabi 'yan majalisa dari biyu da arba'in da tara ne daga cikin 'yan takara fiye da dubu biyu da dari biyar; ana kuma sa ran samun sakamako na farko-farko nan da makwanni uku.

Sai dai masu sa ido a kan zabubbukan na sa ran za a samu dubban korafe-korafe daga 'yan takarar da suka sha kaye, al'amarin da ka iya jinkirta samun sakamakon.