An samu tashe-tashen hankula a zaben Afghanistan

Masu zabe a Afghanistan
Image caption Masu zabe a Afghanistan

A Afghanistan an kammala jefa kuri'a, a zaben majalisar dokokin kasar da aka gudanar a yau.

An sami tashe-tashen hankulan da suka janyo mutuwar akalla mutane goma sha hudu.

A cewar jami'an zabe, an bude fiye da kashi casa'in cikin dari na rumfunan zabe kusan dubu shidda.

Mayakan Taliban, wadanda suka yi barazanar kai hari a kan duk wanda ya shiga zaben, sun ce sun hari rumfunan zabe akalla dari da hamsin: Wani jagoran 'yan adawa, Abdullah Abdullah, ya ce abin takaici ne yadda makiyan Afghanistan suka tayar da hankula a lokacin zaben.

A wajejen karshen watan Oktoba ne ake sa ran samun sakamakon karshe na zabubukan.