Shugabannin Kungiyar ECOWAS na taro a Abuja

Wasu shugabannin kasashen da ke cikin kungiyar ECOWAS ko CEDEAO na yin taron gaggawa a Abuja, tare da jami'an diplomasiyyar kasashen.

Suna dai tattauna wa ne a kan halin da kasar Guinea-Bissau ke ciki, musamman ta fuskar tsaro da kuma siyasa.

Da yake marhabin da wakilai a wajen tattaunawar, Shugaba Goodluck Jonathan ya ce dole ne kasashen yankin su tagazawa makwabciyarsu.

Najeriya ta bayar da shawarar aikewa da dakaru 600 zuwa kasar.

Kasar ta Guinea-Bissau ta shiga cikin halin rudani ne tun bayan da aka kashe shugaban kasar, Joao Bernardo Vieira, a shekarar da ta wuce.

Masu fasa kwaurin miyagun kwayoyi daga kudancin Amurka dake amfani da kasar a matsayin wata kasuwar miyagun kwayoyi da Turai, sun cika kasar ta Guinea-Bissau da kudade.