Goddluck Jonatahan ya kaddamar da yakin neman zabensa

Shafin Facebook na shugaban Najeriya Goddluck Jonathan
Image caption Shafin Facebook na shugaban Najeriya Goddluck Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kaddamar da takararsa, ta neman shugabancin kasar, karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

Dubban magoya bayansa ne dai suka hallara a dandalin Eagle Square dake Abuja, domin bikin kaddamarwar.

A jawabin da ya gabatar, shugaba Goodluck Jonathan ya ce zai tsaya takarar ne da marawar bayan Namadi Sambo a matsayin danatakarar da zai mara masa baya.

Shugaba Jonathan ya ce zai ci gaba da daura wa a kan ayyukan da yake yi a yanzu na ci gaban kasa.

A ranar Alhamis din da ta gabata ce shugaban ya fara bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar, a shafinsa na Facebook.

Taron na yau dai ya samu halartar jiga-jigan jam'iyyarsa ta PDP ciki har da kusan ilahrin gwamnonin kasar da aka zaba karkashin jam'iyyar.

Hakan ya sanya masu nazari na gani da walakin, saboda wasu daga cikinsu sun halarci taron kaddamar da takar Janar Ibrahim Babangida, wanda shi ma ke neman shugabancin kasar.