Rana ta biyu ta ziyarar Fafaroma a Burtaniya

Fafaroma Benedict a birnin Glasgow
Image caption Fafaroma Benedict a birnin Glasgow

Shugaban Cocin Roman Katolika, Fafaroma Benedict, zai halarci taron ibadar mabiya addinin Kirista a yau tare da shugaban Darikar Anglikan na duniya, kuma Archbishop na Canterbury.

Taron ibadar, wanda za a yi a birnin Landan, zai gudana ne a rana ta biyu ta ziyarar da Fafaroman ke yi a Burtaniya.

Hakan na zuwa ne kasa da shekara guda bayan karuwar sa-in-sa tsakanin majami'un biyu lokacin da Fafaroma Benedict ya yanke shawarar sake karbar mabiya Darikar Anglikan din da suka bujirewa darikar tasu.

A jiya Alhamis ne dai Fafaroma Benedict ya bukaci Burtaniya ta yi riko da tushenta na Kiristanci, inda ya kuma ya ce cocinsa ta yi ta jan kafa wajen daukar matakai bayan bayanan da suka bayyana dangane da zargin lalata da aka yiwa wasu daga cikin manyan limaman cocin.