Addinai na fuskantar barazana, in ji Paparoma Benedict

Paparoma Benedict
Image caption Paparoma Benedict

A wani jawabi mai cike da tarihi da yayi a majalisar dokokin Birtaniya, a rana ta biyu ta ziyarar da ya ke a kasar, Paparoma Benedict ya ce ya kamata mabiya addinai, da kuma wadanda ba ruwansu da addini, su fahimci juna domin cigaban dan adam.

Ya ce, wadanda ke neman dakushe tasirin addini, ba su fahimci irin mahimmiyar rawar da addinin ke takawa a rayuwar jama'a ba.

A wani bangare kuma, 'yan sanda masu yaki da ta'addanci sun kama mutum na shidda, dangane da zargin shiryawa Paparoma makarkashiya, a lokacin ziyararsa a Birtaniyar.