Cutar HIV ta ragu a yankin kudu da hamadar sahara na Afrika

Alkaluman da aka saki yanzu-yanzun nan na cewa adadin masu kamuwa da kwayar cutar HIV mai karya garkuwar jiki ya ragu da fiye da kaso daya cikin hudu a cikin shekaru goman da suka gabata a kasashen Afrika da ke kudu da Sahara, inda nan ne cutar ta fi tsanani a duniya.

Alkaluman da hukumar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ta majalisar dinkin duniya ta tattara na nuna cewa kasashe irinsu Ivory Coast, da Habasha, da Najeriya, da Afrika ta kudu, da kuma Zimbabwe suna kan gaba wurin raguwar masu kamuwa da cutar.

Hukumar ta ce kyautata matakan rigakafi da wayar da kan al'uma ne suka haddasa raguwar masu kamuwa da cutar.

Wani kakakin hukumar yaki da cutar AIDS ta majalisar dinkin duniya ya ce a karon farko ana samun sauyi a daidai inda annobar tafi kaifi.

Wata sanarwa daga hukumar ta ce kyawawan matakai da kuma zafafa fadakarwa na taimakawa ga raguwar.

To amma ta kara da cewar, yayinda ake samun ci gabaa yankunan da matsalar tafi kamari, sauran yankuna, kamar gabacin turai da kuma tsakiyar Asiya na bayar da rahoton karuwar annobar.