Sarkozy da Merkel sun yi musayar kalamai

Shugaba Sarkozy na Faransa da Shugaba Angela Merkel ta Jamus
Image caption Shugaba Sarkozy na Faransa da Shugaba Angela Merkel ta Jamus

Korar 'yan kabilar Roma daga kasar Faransa na ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin shugabannin Tarayyar Turai.

Bayan wani taron koli na Tarayyar Turan a birnin Brussels, Shugaba Nicholas Sarkozy na kasar Faransa ya shaidawa wani taron manema labarai cewa bakin kusan dukkan shugabannin Tarayyar ya zo daya kan cewa Kwamishiniyar Shari'a ta Tarayyar Turai, Viviane Reding, ta yi azarbabi da ta kwatanta shawarar da Faransar ta yanke ta korar 'yan kabilar Roma 'yan share-wuri-zauna da yadda 'yan Nazi suka rika tarkata dimbin jama'a lokacin Yakin duniya na Biyu.

Shugaban na Faransa ya kuma ce Shugaba Angela Merkel ta Jamus ta shaida masa cewa a 'yan makwanni masu zuwa ita ma za ta rufe sansanonin 'yan kabilar Roman da ke kasarta.

To amma ga alamu Misis Merkel ba ta ji dadin wadannan kalamai na Mista Sarkozy ba.

Komawarta Berlin ke da wuya, sai mai magana da yawun Shugaba Angela Merkel, Stefan Seibert, ya musanta cewa wata magana a kan ’yan kabilar Roma ta shiga tsakanin shugabar ta Jamus da Mista Sarkozy balle ma har ta ce za ta koresu daga kasarta.

Viviane Reding din dai—wacce ta jawo ce-ce-ku-cen—ta yi barazanar kai Faransa gaban kotun Tarayyar Turai a kan wannan batu.