An yaba da jaruntar 'yan Afghanistan

Layin masu jefa kuri'a a Afghanistan
Image caption Layin masu jefa kuri'a a Afghanistan

Majalisar Dinkin Duniya da rundunar tsaron NATO a Afghanistan sun yaba da jaruntar da mutanen kasar ta Afghanistan suka nuna ta jefa kuri'unsu duk kuwa da tashe-tashen hankulan da suka yi sanadin rasa rayuka.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ne dai, Ban Ki-moon, ya yaba da jaruntar mutanen na Afghanistan.

Shi kuwa kwamandan dakarun NATO, Janar David Petraeus cewa ya yi zaben ya nuna cewa makomar Afghnaistan na hannun 'yan kasar.

Duk da barazanar kungiyar Taliban dai, an kiyasta cewa mutane akalla miliyan uku da dubu dari biyar ne, wato kashi arba'in cikin dari na wadanda suka yi rajista, suka kada kuri'unsu.

Wannan ya nuna cewa yawan mutanen da suka kada kuri'a a zaben majalisar dokokin ya dara na wadanda suka kada a zaben shugaban kasa bara.

An samu tashe-tashen hankula a fadin kasar, inda masu ta da kayar baya suka kai hari a kan rumfunan zabe, da 'yan takara, da kuma masu kada kuri'a; to amma hakan bai hana gudanar da zaben ba.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta ce kusan mutane goma sha hudu ne suka rasa rayukansu, yayinda arba'in da biyar kuma suka yi rauni.

Sai dai an samu rahotannin cewa an tafka magudi, al'amarin da ka iya jawo shakku danganae da sahihancin zaben.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Afghnaistan, Staffan de Mistura, ya bayyana cewa ya yi wuri a ce zaben ya yi nasara.

Karin bayani