Jami'yyar ANPP ta zabi sababbin shugabanni

Image caption Tutar jami'yyar ANPP

Jami'yyar adawa ta ANPP a Najeriya ta zabi Cif Ogbonnaya Onu a matsayin sabon shugabanta.

Ta kuma zabi Dakta Yusuf Musa a matsayin mataimakin shugaban jami'yyar a yayinda Malam Shetima Ari shine sakataren jami'yyar.

Jami'yyar ta kuma zabi Ikienna Ogbuna a matsayin shugaban matasa.

A jiya ne dai jami'yyar ta zabi sababbin shugabannin bayan da ta gudanar da baban taronta a Abuja , babban birnin Najeriya.