'Goodluck Jonathan ya ci da zuci'

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

'Yan siyasa a Najeriya sun fara mayar da martani ga matakin da Shugaba Goodluck Jonathan ya dauka na kaddamar da shirinsa na yin takarar shugabancin kasar a zaben shekarar 2011.

Yayin da wadansu ke ganin shugaban ya yi daidai wajen kaddamar da takarar tasa a inuwar jam'iyyar PDP dai, wadansu kuwa cewa suke yi wannan mataki bai dace ba saboda tsarin jam'iyyar na karba-karba tsakanin kudanci da arewacin kasar.

Ambasada Yahaya Kwande, wani na hannun daman tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, ya ce shugaban na Nijeriya ya yi ci-da-zuci.

“Idan da ya bi ka’idar da ke shimfide, [da ya] yi mamakin yawan mutanen arewan da za su goyi bayansa.

“Amma muna ganin akwai kuskure [a] fitarsa [takara] a yanzu, domin alkawari aka yi”, inji Ambasada Kwande.

Ambasada Yahaya Kwande ya kuma shaidawa wakilin BBC cewa ‘yan siyasar arewa ba yaki suke yi da Shugaba Goodluck ba.

“Abin da muke cewa kawai shi ne yarjejniyar da muka yi a tsaya a kai”.

A halin da ake ciki kuma, bisa ga dukkan alamu yunkurin da wadansu fitattun 'yan takara daga arewan ke shirin yi na fitar da mutum daya daga cikinsu a matsayin dan takarar shugaban kasa ka iya fuskantar koma-baya.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai wata sanarwa, wacce ke dauke da sa hannu shugaban kungiyar yakin neman zaben Janar Ibrahim Babangida da na kungiyar Atiku Abubakar, ta ce wadansu 'yan takarar shugabancin kasar—Janar Ibrahim Babangida da Janar Aliyu Gusau, da Atiku Abubakar, da Bukola Saraki—za su marawa mutum daya daga cikinsu baya.

Sai dai wani jigo a kungiyar yakin neman zaben Janar Aliyu Gusau, Alhaji Aminu Garba Gusau, ya shaidawa wakilin BBC a Kaduna cewa su basu san da wannan zance ba.

“A gaskiya mu ba mu san da wannan magana ba, kuma ba mu yarda da ita ba, kuma ba ma kanta”, inji shi.

Ya kuma ce in dai ana maganar ci gaba da bin tsarin karba-karba ne to kamata ya yi mulkin ya koma bangaren da ya ke zamanin Marigayi Shugaba Umaru ’Yar’aduwa—wato yankin arewa maso yamma.

“Shi mulkin nan fa daga arewa maso yamma ya fito.

“In adalci ake so a yi, in kuma karba-karba ake so a ci gaba da yi, in har ana so mulkin ya dawo arewa, kamata ya yi a mayar da shi gidan da ya fito....

“Su wadannan da aka ce sun fito ko suna so su yi, ba ’yan arewa maso yamma ba ne: ga ka’ida, ga cancanta, ga adalci, kamata ya yi mulkin nan fa ya koma arewa maso yamma”.

Karin bayani