Ranar karshe ta ziyarar Fafaroma a Burtaniya

Fafaroma Benedict
Image caption Fafaroma Benedict a Burtaniya

Fafaroma Benedict yana birnin Birmingham a rana ta karshe ta ziayarar aikin da ya ke yi a Burtaniya.

Cocin Katolika dai na kallon wannan rana ta yau a matsayin kololuwar gabaki dayan ziyarar ta Fafaroma.

Fafaroman zai tsarkake wani masanin addinin Kirista na karni na goma sha tara, Cardinal Newman, wato zai daukaka matsayinsa zuwa 'Mai Albarka'.

A Dandalin Crofton—inda za a yi addu’o’in—za a gabatar da John Henry Newman a matsayin wani gwarzo wanda ya cancanci mabiya darikar Katolika su yi koyi da shi.

An kiyasta cewa mutane dubu sittin ne za su halarci addu'o'in, ko da yake wannan kiddigar ba ta kai wacce aka yi tun farko ba ta yawan mutanen da za su halarta.

Wannan kalubale da darikar ta Katolika ke fuskanta na raguwar mabiya kuma zai kara bayyana daga bisani lokacin da Fafaroman zai ziyarci makarantar horar da limaman coci ta Oscott, wadda ke shan wahala wajen samun daliban da za ta horar.

Fafaroman zai kare ziyarar tasa ne da wani jawabi ga bishop-bishop din Ingila, da Scotland, da Wales.

Karin bayani