An fitar da sakamakon zaben Sweden

Image caption Firaministan Sweden Fredrik Reinfeldt

Wata jam'iyyar masu ra'ayin rikau na yan mazan jiya ta yi nasarar shiga majalisar dokokin Sweden, tare da hana kawancen jam'iyyu masu sassaucin ra'ayin mazan jiya da ke mulkin kasar samun cikakken rinjaye.

Jam'iyyar ta Sweden Democrats wacce ta yi kamfe akan batun hana baki shiga kasar, a zaben da aka gudanar jiya Lahadi ta yi nasarar samun kaso shida na kuri'un da aka kada inda ta samu wakilai ashirin a majalisar.

Kawancen jam'iyyun da ke mulki karkashin jagorancin firaminista Fredrik Reinfeldt, sun gaza samun cikakken rinjaye inda suka samu kaso arba'in da tara na kuri'un da aka kada.

Tuni dai shugabar jami'yyar Social Democrats Nona Sahalin ta amince da sakamkon zaben.