Mahimman abubuwan da suka faru a Najeriya

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Shekaru 800 kafin haihuwar Annabi Isa : Kabilar Nok sun zauna a garin Jos, tun kafin a samu wayewa irinta zamani.

Karni na 11 zuwa sama: Aka kafa garuruwa, da masarautu, ciki harda masarautun kasar Hausa data Borno a Arewacin kasar, da masarautun Oyo da Benin a Kudu.

1472 – Turawan Potugal suka iso gabar ruwan Najeriya.

Karni na 16-18th - Cinkin bayi: An tura miliyoyin ‘yan Najeriya zuwa Amurka a matsayin bayi ta karfi da yaji.

1809 – Aka kafa daular musulunci ta Sokoto – karkashin jagoranjcin Sheikh Usman Dan Fodiyo a Arewacin kasar.

1830s-1886 – Yakin basasa ya barke a kasar Yarbawa dake kudancin kasar.

1850s – Turawan Burtaniya suka fara kafa matsugunansu a yankin Legas.

1861-1914 – Burtaniya ta kara karfafa ikonta kan abinda ta kira yankin Najeriya, ta hanyar mulki ta bayan fage, tare da yin amfani da sarakunan gargajiya a matsayin shugabannin al’umma.

1922 – Aka kara wani bangare na kasar Kamaru mallakin Jamus a Najeriya, sakamakon umarnin kungiyar League of Nations.

1960 – Samun ‘yancin kai, inda Fira Minista Sir Abubakar Tafawa Balewa, ya jogoranci gwamnatin hadin Kan kasa.

1962-63 – Kididdigar jama’a mai cike da rudani ta haifar da rikice-rikicen kabilanci da bangaranci.

1966 Janairu – aka kashe Abubakar Tafawa Balewa a wani juyin mulki. Inda Manjo-Janar Johnson Aguiyi-Ironsi ya zama shugaban gwamnatin soji.

1966 Juli – Aka kashe Janar Ironsi a wani juyin mulkin na daban, inda aka maye gurbinsa da Lieutenant-Colonel Yakubu Gowon.

1967 – Jihohi uku na Gabashin kasar suka balle domin kafa kasar Biafara, abinda ya haifar da yakin basasa.

1970 – Shugabannin Biafara suka mika wuya, aka maida yankin zuwa tarayyar Najeriya.

1975 – Aka kifar da gwamantin Gowon, sannan ya gudu zuwa Burtaniya, inda aka maye gurbinsa da Brigadiya Murtala Ramat Mohammed, wanda ya fara shirin maida babban birnin kasar zuwa Abuja.

Obasanjo – a karon farko

1976 – An kashe Mutala Mohammed a wanin juyin mulki da baiyi nasara ba, inda aka maye gurbinsa da mataimakinsa Lieutenant-Janaral Olusegun Obasanjo, wanda ya taimaka wajen bullo da tsarin shugabanci irin na Amurka.

1979 – Aka zabi Alhaji Shehu Shagari a matsayin shugaban kasa a wani zabe da aka gudanar na kasa baki daya, wanda ya haifar da jamuhuriya ta biyu.

1983 Janairu – gwamnati ta kori dubban daruruwan ‘yan kasashen waje, mafiya yawansu ‘yan kasar Ghana, tana mai cewa sun haura adadin zamansu a kasar, kuma suna tare guraban ayyukan da ‘yan kasar ya kamata su samu. An dai yi Allah wadai da matakin a kasashen waje, amma ya samu karbuwa a cikin gida.

1983 Augusta, Satumba – aka sake zabar Shagari a karo na biyu, sai dai an yi zargin tafka magudi.

1983 Disamba - Manjo-Janar Muhammad Buhari ya kwaci mulki a wani juyin mulkin da ba’a zubda jini ba.

1985 - Ibrahim Babangida ya kwaci mulki a wani juyin mulkin da ba’a zubda jini ba.

1993 Juni – Sojoji suka soke zaben shugaban kasa, bayanda sakamako ya nuna cewa Cif Moshood Abiola ne kan gaba wajen lashe zaben.

1993 Agusta – aka mika mulki ga gwamnatin rikon kwarya.

Mulkin janar Abacha

1993 Nuwamba - Janar Sani Abacha ya kwaci mulki, sannan ya takure ‘yan adawa.

1994 – An kama Abiola bayanda ya bayyana kansa a matsayin shugaban kasa.

1995 – aka kashe Ken Saro-Wiwa, ewani mai fafutukar kare hakkin yankin Ogoni bayan wata shari’a da aka yi masa mai cike da suka. A martanin data mayar, tarayyar Turai ta sakawa kasar takunkumi har zuwa shekarar 1998, sannan kungiyar kasashen Commonwealth ta dakatar da Najeriyar.

1998 – Allah ya yiwa janar Abacha rasuwa, inda Manjo-Janar Abdulsalami Abubakar ya maye gurbinsa. Yayinda Cif Abiola ya rasu a gidan yari wata guda bayan hakan.

1999 – An gudanar da zaben kasa baki daya, sannan aka rantsarda Olusegun Obasanjo a matsayin shugaban kasa bayan ya lashe zaben.

2000 – Wasu jihohi sun fara aiki da tsarin shari’ar musulunci a Arewacin kasar duk da rashin amincewar da mabiya wasu addinai suka nuna. Hakan kuma ya haifar da rikice-rikice a sassa da dama.

2001 – Rikicin kabilanci a jihar Benue ya haifar da asarar rayuka da dama, tare da raba dubbai da gidajensu.

Sannan a watan Oktoba, sojoji suka kashe fararen hula fiye da 200, bayanda aka tura su domin shawo kan matsalar, a wani abu da akewa kallon ramuwar gayya ce bisa sojoji 19 da aka kashe.

2001 Oktoba – Shugaba Olusegun Obasanjo na Najeriya, da Mbeki na Afrika ta Kudu da Bouteflika na Aljeriya suka kaddamar da shirin ciyar da nahiyar Afrika gaba wanda aka yiwa lakabi da New Partnership for African Development, ko kuma Nepad, wanda ya kunshi daina yaki domin samun taimako da kuma zuba jari da fitar da kayayyakin da nahiyar ke samarwa.

Rikicin kabilanci

2002 Fabreru – Kimanin mutane 100 aka kashe a birnin Lagos, a wani rikici da ya barke tsakanin Hausawa da yarbawa. Dubban jama’a ne suka bar gidajensu.

2002 Nuwamba – Fiye da mutane 200 aka kashe bayanda rikici ya barke a garin Kaduna, sakamakon shirin gabatar da zaben sarauniyar kyau. Daga bisani an mayar da bikin zuwa Burtaniya.

2003 12 ga watan Aprilu – Aka gudanar da zaben farko bayan tafiyar sojoji a 1999.Sai dai zaben ya sha suka bisa zargin magudi da satar kuri’a da jinkiri. Jam’iyyar PDP ta shugaba Obasanjo ce ta samu kujeru masu rinjaye a majalisar dokokin.

Sake zaben Obasanjo

2003 19 Aprilu – an gudanar da zabe karkashin jagorancin farar hula tun bayan kawo karshen mulkin soji, kuma an zabi Obasanjo a matsayin shugaban kasa karo na biyu da kusan kashi 60 cikin dari. Jam’iyyun adawa sun yi watsi da sakamakon zaben. Masu sa ido na kungiyar Tarayyar Turai sun ce “an kaucewa ka’idoji da dama”.

2003 Yuli – An kawo karshen yajin aikin da aka shafe kwanaki 9 ana yi bayanda gwamnati ta amince ta saukaka farashin man data kara.

2003 Augusta – Wani rikicin kabilanci a garin Warri na jihar Delta dake yankin Niger Delta mai arzikin mai yayi sanadiyyar rayukan jama’a fiye da 100, yayinda wasu 1000 suka samu raunuka.

2003 Satumba – Aka harba tauraron dan ‘adam na farko na Najeriya, ta hanyar tauraron kasar Rasha.

2004 Janairu – Majalisar dinkin duniya ta kawo karshen cece kuce kan mallakar iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru, inda kasashen biyu suka yi alkawarin yin sunturi tare akan iyakokinsu.

2004 Mayu – An kafa dokar tabaci a jihar Plato bayanda aka kashe fiye da musulmai 2000 a garin Yelwa a wani hari da mabiya addinin kirista suka kai musu. Sannan aka kai wasu hare-haren ramuwar gayya a garin Kano.

Tashin hankali a Kudu

2004 Augusta-Satumba – Rikici tsakanin kungiyoyin asiri a garin fatakwal ya sa sojoji sun kai sumame abinda kuma yayi sanadiyyar mutuwar mutane 500 a cewar kungiyoyin kare hakkin bil’adama, sai dai gwamnati ta ce mutane 20 ne suka rasu.

2005 Yuli – Kungiyoyin bada bashi na Paris Club suka amince su yafewa Najeriya kashi biyu cikin uku na bashin da suke binta, wanda yawansa yakai dala biliyan 30.

2006 Janairu zuwa sama – Masu fafutuka a yankin Niger Delta suka kai hari kan wuraren hakar mai tare da yin garkuwa da ma’aikata ‘yan kasashen waje. Suna dai bukatar samun karin iko ne da albarkatun man da ake hakowa a yankin nasu.

2006 Febreru – Fiye da mutane 100 aka kashe a rikicin addini da ya barke a arewacin kasar da kuma garin Onitsha dake kudu.

2006 Aprilu – tare da taimakon kudaden shiga na man fetur, Najeriya ta zaman kasa ta farko a Afrika data biya bashin da kasashen Paris Club ke binta.

2006 Mayu – Majalisar dattawa ta yi watsi da kudurin dake neman a sauya kundin tsarin mulki domin baiwa shugaba Obasanjo damar zarcewa kan karagar mulki a zaben shekara ta 2007.

Yarjejeniyar Bakassi

2006 Augusta – Najeriya ta amince ta mika iko ga Kamaru na yankin Bakassi, bayan wani hukunci na kotun duniya a shekara ta 2002. An kafa wata hukuma ta musamman ta farar hula da za ta shugabanci yankin cikin shekaru biyar.

2006 Oktoba – Wani hadarin jirgin sama ya kashe Sarkin musulmi mai alfarma Maccido, wanda shi ne hadarin jirgi na uku mafi muni da ya faru a kasar cikin shekara guda.

2007 Aprilu – An bayyana Umaru Yar'Adua na jam’iyyar PDP mai mulki a matsayin wanda ya lashe zaben kasar da aka gudanar.

2007 Satumba – Kungiyar masu fafutukar ‘yanto yankin Niger Delta, Movement for the Emancipation of the Niger Delta, ta yi barazanar kawo karshen tsagaita wuta na kashin kai data yi, tare da kai sabbin hare hare kan wuraran hakar mai.

2007 Nuwamba – wasu ‘yan bungida da ake zargin sun fito daga Najeriya sun hallaka sojojin Kamaru 21 a yankin Bakassi.

Majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da matakin da gwamnati ta dauka na mika yankin Bakassi ga kasar Kamaru.

2007 Disamba – Aka maida shugaban hukumar yaki da cinhanci da rashawa Nuhu Ribadu saniyar ware, sai dai jim kadan sai hukumar ta gudanar da wasu manyan kame kame.

Farashi ya tashi

2008 Janairu – farashin danyan mai ya kai dala 100 a karon farko a tarihi, yayinda rikici a kasashe irinsu Najeriya da Aljeriya suka kara ingiza farashin.

2008 Fabreru – Hukumomi a Angola suka mikawa Najeriya shugabannin kungiyar Mend Henry Okah da Edward Atata, wadanda ake zargi da laifin kai hare hare a yankin Niger Delta.Rahotannin da suka nuna cewa an kashe Okah a kurkuku sun bayyana cewa na kanzon kurege ne.

Kotun kula da korafe korafen zabe ta amince da zaben shugaba Umaru Yar'Adua, wanda masu hamayya suka nemi a soke, bisa zargin magudi.

2008 Aprilu – An zargi wasu tsaffin ministocin lafiya biyu da diyar shugaba Obasanjo cikin wasu manyan ma’aikatan lafiya 12 da almubazzaranci da dukiyar jama’a da yawanta yakai dala miliyan 4.

An rage yawan adadin man da ake hakowa da rabi sakamakon hare hare kan wuraren hakar man da kuma yajin aiki; matsalar da tasa farashin man a duniya yayi tashin gwauron zabo.

2008 Augusta – Biyo bayan yarjejeniyar da aka cimma a watan Maris Najeriya ta mika yankin Bakassi ga Kamaru, abinda ya kawo karshen tashin hankalin da aka dade ana yi.

Kasar ta amince ta taimakawa Najeriya da makamashin nukiliya domin inganta hasken wutar lantarki.

2008 Satumba – masu fafutuka a yanikin Niger Delta sun kara kaimi kan hare haren da suke kaiwa; sakamakon harin da sojoji suka kai a sansaninsu.

Farashin mai ya fadi

2008 Oktoba- gwamnati ta rage kasafin kudin kasar sakamakon faduwar farashin mai.

2008 Nuwamba – Akalla mutane 200 ne aka kashe sakamakon rikici tsakanin musulmai da kirista a garin Jos da ke tsakiyar kasar.

2009 Janairu – Kungiyar masu fafutuka ta Mend, ta kawo karshen tsagaita wutar da ta yi na watanni hudu, bayanda sojoji suka kai hari kan wani sansanin wata kungiya dake kawance da ita.

2009 Maris –wasu jam’iyyu 19 suka bada sanarwar hadewa wuri guda domin kafa jam’iyyar MEGA da nufin kalubalantar jam’iyyar PDP a zaben 2011.

2009 Mayu – Masu fafutuka a yankin Niger Delta na kungiyar Mend suka yi watsi da shirin gwamnati na yi musu afuwa, sannan suka sha alwashin ci gaba da kai hare-hare.

2009 Yuli – An kashe daruruwan mutane bayanda kungiyar Boko Haram ta bayyana a yankin arewacin kasar, da nufin tabatar da tsarin shari’a da kuma Allah wadai da tsarin karatun boko. Jami’an tsaro sun kai hari kan mazaunar kungiyar sannan suka kashe shugabansu.

Gwamnati ta saki shugaban kungiyar Mend, Henry Okah, bayanda ya karbi shirinta na afuwa.

2009 Augusta – Shirin ahuwar da gwamnati ta bayyana na watanni biyu ya fara aiki gadan-gadan.

Tafiyar shugaba ‘Yar’adua

2009 Nuwamba - Shugaba Yar'Adua ya tafi zuwa Saudi Arabiyadomin yi masa magani kan ciwon zuciyar da yake fama da shi. Sai dai dadewar da yayi ta haifar da rikicin tsarin mulki, inda wasu suka yi kira a gareshi da ya sauka.

2010 Janairu – Akalla mutane 149 ne aka kashe a wani rikici da ya barke tsakanin musulmi da kirista a garin Jos.

2010 Febreru- Majalisun dokoki sun amincewa mataimakin shugaban kasa Goodluck Jonathan ya zamo mukaddashi, har sai shugaba ‘ya’adua ya murmure.

Alhaji Yar'Adua ya dawo Najeriya amma bai ci gaba da aiki ba.

2010 Maris – Fiye da mutane 120 ne aka kashe a wani sabon rikicin da ya kara barkewa tsakanin musulmi da kirista a garin Jos.

Mukaddashin shugaban kasa ya kori baki dayan majalisar zartarwa ta kasar a wani mataki na karfafa ikonsa.

2010 Aprilu - Mukaddashin shugaban kasa Goodluck Jonathan ya rantsar da sabuwar majalisar zartarwar kasar.

Jonathan ya zama shugaban kasa

2010 Mayu – Allah ya yiwa shugaba Umaru Yar'Adua rasuwa bayan doguwar jinya. Kuma an rantsar da mataimakinsa, Goodluck Jonathan, wanda tuni dama yake aiki a madadinsa a matsayin cikakken shugan kasa.