Mazauna Asuboi na fama da dundumi

Rahotannin da ke fitowa daga garin Asuboi na jihar Ashanti a kasar Ghana, sun ce baki dayan mazauna garin na fuskantar barazanar kamuwa da cutar makanta.

Hakan dai yana da nasaba mamayar da kudan tsando ya yi masu, wanda kuma yake haddasa cutar dundumi, mai sa mutum ya makance. Rahotannin sun kara da cewa hakan ya sa kusan dukkan mazauna wannan gari na Asuboi na fama da kuraje a jikinsu, sanadin cizon da kudajen tsandon ke yi mu su.

Hukumomi a yankin na cewa suna daukar matakai, domin agaza wa mazauna wannan gari, domin yaki da wannan cuta wadda ke sa launin fatar wasu daga cikinsu na sauyawa.